Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Bayan Samun Gagarumar Riba Bankin Jaiz Zai Fadada Rassa A Nijeriya

Daga Auwal Adam  Bankin kasuwanci na Jaiz a Nijeriya, ya sanar da samun riba kafin haraji na Naira biliyan 3 da miliyan 700 a sh...

Daga Auwal Adam 

Bankin kasuwanci na Jaiz a Nijeriya, ya sanar da samun riba kafin haraji na Naira biliyan 3 da miliyan 700 a shekarar 2020, wanda ke nuna samun karin kashi 45.31 cikin dari da ke matsayin sama da Naira biliyan 2 da miliyan 100 da bankin ya samu a 2019.

Jumullar kudaden shiga da Bankin na Jaiz ya samu kamar yadda Rahoton kasafin shekarar da ta ƙare a ranar 31 ga watan Disambar 2020 ya nuna, ya samu haɓakar kashi 33.29 daga Naira biliyan 14 da miliyan 700 da 1 a 2019 zuwa Naira biliyan 19 da miliyan 600 a 2020.

Jumullar kadarori ko Jarin da bankin ya mallaka a yanzu ya kai naira biliyan 233 da miliyan 59 sabanin naira biliyan 167 da miliyan 27 da ya mallaka a 2019 alkaluman da ke nuna samun tagomashin kashi 40.

Haka ya nuna karuwar riba bayan haraji daga Naira biliyan 2 da miliyan 44 cikin shekarar da ta gabata zuwa Naira biliyan 2 da miliyan 90 na shekarar da ta ƙare.


Alkaluman na 2020 ya sake tabbatar da yanayin ci gaban da bankin marar ruwa ya gani a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Shugaban Bankin, Mr Hassan Usman ya ce dabarun bunkasa bankin ya mayar da hankali ne kan hakikanin bangaren tattalin arziki, musamman kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs) da cibiyoyin hada hada-hadar kudade.

A cewar Mr Hassan Usman Bankin zai ci gaba da fadada ayyukansa a sassan Najeriya ta hanyar bude rassa tare da amfani da fasahohin zamani wajen kaiwa ga kasuwannin da ya ke buri a fadin kasar da kuma janyo hankalin abokanan hulda.

No comments