Buhari Ya Dage Tafiyarsa Zuwa LandanBBC Hausa ta labarto cewa; shugaban kasa Muhammaduu Buhari ya ɗage tafiyar da zai yi a yau Juma'a zuwa Landan.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar ta ce za a sanar da ranar tafiyar a nan gaba.

Sai dai Femi Adesina bai bayar da dalilin ɗaga balaguron ba.

Da yammacin Alhamis ne Fadar Shugban Ƙasa ta ce Shugaba Buhari zai je birnin Landan na Ingila domin duba lafiyarsa.

Kusan wata uku kenan rabon da shugaban ya je wurin likitocin nasa, inda ya je ranar 30 ga watan Maris.

Balaguron Buhari zuwa Landan na jawo cecekuce a kowane lokaci. Wasu 'yan Najeriya mazauna birnin sun yi zanga-zanga a ƙofar masaukinsa yayin zuwansa na ƙarshe.

Post a Comment

0 Comments