CAN Ta Ce Ƴan Nijeriya Na Fama Da Yunwa Da Rashin TsaroBbc Hausa labarto cewa; Kungiyar Kiristocin Nijeriya wato CAN reshen arewacin kasar ta ce tabarbarewar tsaro da kuma matsin tattalin arziki ya jefa miliyoyin yan Najeriya cikin yunwa da talauci.

CAN ta ce ba ta ga alfanun bikin ranar demokradiyya ba da aka yi a ranar 12 ga watan Yuni, la'akari da yadda ake ci gaba da satar dalibai da kuma hana manoma shiga gonakinsu, wanda kungiyar tace zai haifar da yunwa a nan gaba.

Jaridar The Nation ta ambato kakakin kungiyar reshen arewa, Rabaran Jechonia Albert na cewa ''CAN ta damu da yadda hare-hare ke karuwa a makarantu, da kuma satar dalibai musamman a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da kuma Neja.

A makonnin da suka gabata ne wasu mahara suka sace daruruwan daliban makarantar Islamiyya a garin Tegina na jahar Neja.

Shugaba Buhari a jawabinsa na ranar demokradiyya ya sha alwashin tabbatar da gwamnatinsa ta kawo karshen hare-haren 'yan bindiga.

Post a Comment

0 Comments