Daliban Jami'ar KASU a yau Talata sun ci gaba da zanga-zanga kan karin kudin makaranta da gwamnatin APC ta jihar Kaduna wacce El-Rufai ke jagoranta ta yi.
Daliban sun gudanar da salloli a tsakiyar titin Kaduna, inda kuma suka rufe duk wani babban hanya da zai sada mutum da gidan gwamnatin Kaduna ta Sir Kashim Ibrahim.
Daliban na neman a rage kudin makarantar, inda suka yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya sanya baki domin a samu a rage musu kudin makarantar.
Ga yadda zanga-zangar ta gudana cikin hotuna:
0 Comments