Daliban Jami'ar KASU Sun Ziyarci Jami'ar Maryam Abacha Ta KanoWadansu daga cikin daliban sashen ilimin kimiyyar kasa wato 'Geography' na Jami'ar jihar Kaduna a ranar Alhamis sun kai ziyara Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya  (MAAUN) dake Kano. 


Daliban sun kasance karkashin jagorancin Farfesa Lar daga sashen 'Geography', an kuma zagaya da su cikin Jami'ar ta Maryam Abacha American University, dake Hotoro a cikin kwaryar Kano. 


A yayin ziyarar, an zagaya da daliban sun ga tsangayoyi daban-daban da ake da su a jami'ar da kuma dakunan bincike na ilimi, ajujuwan karatu, dakin karatu, da kuma dakin kwanan dalibai da sauran wurare masu muhimmanci dake cikin jami'ar. 


A bayaninsu, daliban sun jinjinawa shugaban Jami'ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa assasa wannan jami'ar a cikin garin Kano mai tarihi tare da sanya dimbin kayayyaki a cikin jami'ar. 


Har wala yau a na shi jawabin, Farfesa Lar ya bayyana jindadinsa ga shugaba kuma mu'assasin Jami'ar ta MAAUN ta Maradi dake jamhuriyyar kasar Nijer da ta Kano a Nijeriya. 


Sannan ya jinjinawa Farfesa Abubakar Gwarzo bisa kwazon da ya nuna wajen samar da Jami'ar Franco-British International University dake Kaduna.


Farfesa Lar ya yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa shugaban Jami'ar ta MAAUN bisa yadda ya rika bai wa jami'o'in Nijeriya gudummawar motoci kirar bas-bas tare da bai wa dalibai damar karatu kyauta musamman masu kwazo a cikinsu da kuma marasa karfi. 


"Gaskiya wannan gudummawa ya cancanci jinjinawa tare da zama abin alfahari ga dukkanin 'yan Nijeriya", inji shi. 

Post a Comment

0 Comments