Dalilan Da Ke Haddasa Faduwa Jarrabawar “JAMB” - Daga Aliyu Dahiru Aliyu

Aliyu Dahiru Aliyu, marubucin makalar.


Idan ka yi JAMB a 2005 ko 2010 lokacin da ake turo maka satar amsa ta “text message” a fada maka “type A” ce ko “type C”, yana da kyau yanzu ka gane babu wannan damar domin babu dalibin da yake sanin wace tambaya za a yi masa sai ya bude kwamfuta. 

Idan kana iya leke ka saci amsar dan uwanka a 2002 ko 2008, ka sani yanzu babu wannan damar domin ko ka leka ba abin da zaka gani tun da wanda za ka leka din yana amsawa amsar take gogewa da ya bude wani shafin. 

Idan a 2005 ko 2012 ana siyawa “invigilators” leman kwalba don su kara muku lokaci, a yanzu babu wannan damar tun da lokacinka na cika kwamfuta za ta rufe. Ko dakika daya ba za a kara maka ba. 

Kai yar damar satar amsar ma yanzu babu. A wajejen 2007, malami ne yake zagayawa domin ya hango masu satar amsa. A yanzu kuwa kyamarori ne suke haskoka. Kana satar amsa za a kamaka a ce ka fadi jarrabawa. 

Kuma me yasa ma kuka cire rashin tsaro daga cikin matsalolin? A yanzu daliban sakandare, musamman ta kwana, a firgice suke kada a sacesu. 

Na san da yawa da aka ce su dawo gida saboda fargaba. Ga kuma korona da ta hana karatu. Duk wadannan matsaloli ne manya. 

Ku dena zargin Arewa 24 ko TikTok da faduwa jarrabawar yaran nan. Akwai dalilai da yawa da ya kamata a duba sosai ba zargin wata tasha ba. Zamaninmu duk da su Facebook da 2go, kuma wasu sun ci wasu sun fadi. 

Ni nafi dora laifin a kan makarantu da malamansu. Hukumar JAMB tana saka manhajar karatunta a littattafan da ake kira “brochure and syllabus”, amma makarantu basa amfani da shi. Kawai sai dai su koya abin da suka ga dama kuma su ce dalibi ya shiga jarrabawa da wannan ilimin. 

Wasu makarantun ma ba karatun ake ba. Wasu kuma dalibansu har su zo yin jarrabawar basu iya amfani da kwamfuta ba. Ka gaya min ta yaya za su ci? A iya juya “mouse” ko saka lambar jarrabawa sai lokacin jarrabawar ya wuce! 

Tare da cewa na yi daya daga cikin makarantun da aka tabbatar suna fitar da dalibai masu kokari (GTC Kano), amma ban tsaya iya abin da suke koya min ba. 

Sai da na dinga yawon “lesson” guri-guri kuma ina bin duk abin da ba a koya min ba a makaranta ina samun wani ya koya min duk don na ci JAMB. 

Kuma bara na fada muku, lokacin da na yi JAMB ana tashen ZEE AFLAM kamar yadda ake na Arewa 24 a yanzu. Kumma kullum sai na kalli fim din Indiya a tashar. 

Amma duk bai hanani cin jarrabawa ba saboda na ajiye nishadi a wajensa. Ina zaton tsabagen yin 2go har Master na zama amma ban fadi ba. 

Talabijin ko waya ba su ne manyan musabbaban faduwa jarrabawa ba. Don na tabbata yanzu da za ka ga gidansu wanda ya fi kowa cin jarrabawar sai ka ga watakila talabijin din gidansu har da NETFLIX ma.


Post a Comment

0 Comments