Dan Ta'adda Ya Kashe Mutum Uku A Jamus

 


Wani dan ta’adda dauke da wuka ya kashe mutane tare da jikkata wasu da dama a birnin Wurzburg dake kudancin Jamus a ranar Juma’a.

Majiyarmu ta gidan rediyon Faransa ta labarto cewa; cikin sanarwar tabbatar da kai harin da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar ‘yan sandan kasar ta Jamus ta ce jami’anta sun yi nasarar kama dan ta’addan bayan harbinsa da suka yi a kafa.

Sai dai kafin ya shiga hannu sai da mutumin ya halaka mutane akalla uku tare da jikkata wasu 6 a birnin na Wurzburg.

Har yanzu dai hukumomin tsaron Jamus ba su yi karin bayani kan dan ta’addan ba da kuma dalilinsa na kaiwa fararen hula farmaki.

 

Post a Comment

0 Comments