Ebrahim Raisi Ya Lashe Zaɓen Shugaban Kasa A Iran

 


Babban masanin shari'ar nan na kasar Iran, Ebrahim Raisi, ya lashe zaɓen shugaban kasar.

Sai dai har yanzu ba a bayyana nasararsa a hukumance ba.

Amma ma'aikatar cikin gida ta ce bisa la'akari da yawancin kuri'un da aka kidaya, Mista Raisi ne kan gaba.

Tuni manyan abokan hamayyarsa a takarar shugaban kasa suka taya shi murna.

Post a Comment

0 Comments