Tawagar Belgium ta yi nasarar doke Portugal mai rike da kofin nahiyar Turai da ci 1-0 mai ban haushi, kuma ta samu kaiwa wasan daf da na kusa da na karshe Quarter Finals.
Kwallo daya tilo da Thorgan Hazard yaci a mintuna na 41 kafin tafiya hutun rabin lokaci ya baiwa Belgium din nasara.
Da wannan nasara tawagar Roberto Martinez za ta kara da Italiya a wasan quarter finals ranar Juma'a a Jamus, a ranar Asabar Italiya ta doke Austria da ci 2-1 ta kuma haye matakin.
Jamhuriyar Czech.
Jamhuriyar Czech kuwa ta fitar da ta Netherlands ne bayan doke ta da ci 2 – 0, a wasan na ranar Lahadi.
Da ‘yan wasa 10 Nethelands ta karkare wasan da ta sha kashi, bayan da dan wasanta Matthijs de Ligt ya karbi jan kati, sakamakon tare kwallo da hannu, wanda na’urar taimakawa alkali VAR ta tabbatar kafin daukar matakin.
Da wannan sakamakon Jamhuriyar Czech za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe da Denmark ranar Asabar mai zuwa.
Denmark ta doke Wales da ci 4 da nema a ranar Asabar ta kuma haye wasan quarter finals.
0 Comments