Faransa Ta Samu Maki Uku Da Kyar A Hannun Jamus Da Ci 1 - 0Faransa dake rike da kambin kofin duniya ta fara wasannin gasar Euro 2020 da kafar dama, bayan da ta lallasa Jamus da ci 1-0, sakamakon kwallon da Mats Hummels ya ci kansu a fafatwa mai zafi da sukayi na rukunin F a ranar Talata.

Hummels - wanda aka kira shi don buga wannan gasa ya karasa aikin da Lucas Hernandez ya yi, wajen zuruwa ragarsu kwallo da kansa a mintuna 19 da soma wasar da ya burge ‘yan kallo a Munich.

Alkalin wasa yaki amincewa da wani kwallo da Paul Pogba ya aika kuma Kylian Mbappe ya mikawa Karim Benzema ya karasa raga, amma yace satar fage ne.

Haka ma wani kwallo da Klian Mbappe ya ci, shima aka hana, a matsayin satar fage wato offside.

Nasarar Faransa na nufin su da Portugal, wadanda suka doke Hungary 3-0 a Budapest, sun dauki matakin farko a rukunin F.

Post a Comment

0 Comments