Fusatattun Matasa Sun Kashe Magidanci Da Duka A Jigawa - 'Yan SandaGidan Rediyon Sawaba ya labarto cewa; rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta ce wasu fusatattun matasa sun lakadawa Hasan Sale mai shekaru 40 da ake zarginsa da sata, inda suka yi masa dukan kawo wuka da ya yi ajalinsa. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a yau a Dutse.

Shisu Adam ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a kauyen Chandan da ke karamar Hukumar Birnin Kudu lokacin da wanda ake zargin ya yi kokarin kutsawa cikin shagon sayar da kayayyaki.

Marigayin ya shiga hannun mai shagon ne, wanda ya yi masa ihun da ya jawo hankalin mazauna kauyen.

An lakada masa kazamin duka inda aka garzaya da shi zuwa babban asibitin Birnin Kudu don kula da lafiyarsa amma ya mutu yayin da yake karbar magani a ranar 14 ga Yuni.

Kakakin 'yan sanda ya ce ana ci gaba da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Post a Comment

0 Comments