Shugaban ‘yan adawar haratamtacciyar kasar Israila Yair Lapid ya sanar da cewar ya kafa wata sabuwar kawancen da za ta kawar da Firaminist...
Shugaban ‘yan adawar haratamtacciyar kasar Israila Yair Lapid ya sanar da cewar ya kafa wata sabuwar kawancen da za ta kawar da Firaminista Benjamin Netanyahu daga karagar mulki wanda ya kunshi Jam'iyyar Larabawan dake kasar.
Da zaran Majalisar dokoki ta tabbatar da adadin yawan ‘yan Majalisun da suka goyi bayan wannan sabuwar kawancen, matakin zai kawo karshen mulkin shekaru 12 na Firaminista Netanyahu wanda ke fuskantar zargin almundahana da zamba cikin aminci da kuma cin hanci da rashawa.
Sanarwar Yair Lapid na zuwa ne jim kadan kafin cikar wa’adin karfe 12 na daren jiya Laraba, bayan an dauki dogon lokaci ana tattaunawa da Jam’iyyun adawa daban-daban wadanda ke da fatar ganin an kawo karshen jagorancin Netanyahu.
Lapid ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta yiwa kowanne dan haramtacciyar kasar Israila aiki, tsakanin wadanda suka zabe ta da wadanda ba su zabe ta ba idan ta hau karagar mulki.
A karkashin wannan sabuwar kawancen, Naftali Bennett mai shekaru 49 zai zama Firaminista na farko a yarjejeniyar da za a dinga musayar mukamin, yayin da Lapid zai karbi kujerar bayan shekaru 2.
Bennett ya shaidawa shugaban kasa Reuven Rivlin cewar da taimakon Ubangiji za su yi aiki tare domin yiwa haramtacciyar kasar Israila aiki bayan ya shaidawa duniya samun nasarar kafa kawancen da zai kai shi karagar mulki.
Ana saran nan da mako guda Majalisar dokokin Israila ta kada kuri’ar amincewa da sabuwar kawancen abin da zai ba ta damar karbar mulki.
Firaminista Netanyahu ya bayyana sabuwar kawancen a matsayin mai hadari ga zaman lafiyar haramtacciyar kasar Israila.
-Rahoton RFI Hausa/Madogara
No comments