Gwamnan Jihar Borno
Babagana Umara Zulum ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin sa kai
na kasashen duniya da karkata kashi 30 na kudaden da masu bada agaji ke samarwa
domin tallafawa mutanen da rikicin Boko Haram ya rutsa da su a arewa maso
gabashin kasar kamar yadda RFI Hausa ta labarto.
Zulum wanda ya yi
wannan zargi lokacin da ya karbi Jakadun Amurka da Birtaniya a ofishinsa ya
bukace su da su dinga sanya ido sosai kan kudaden da kasashen su ke bayarwa a
matsayin agaji domin tallafawa mutanen dake bukatar taimako.
Gwamnan ya ce
duk da yake suna gabatar da makudan kudade a matsayin agaji, amma kashi 30 na
kudaden basa zuwa wajen mutanen da aka ware domin su, abin da ya sa ya zama
wajibi a dinga bin irin wadannan tallafi sau da kafa domin sanin inda suke
shiga.
Jakadiyar Amurka
Mary Leonard da ta Birtaniya Catriona Laing sun gana da masu ruwa da tsaki
wajen aikin agaji a Jihar Borno dangane da ayyukan da suke yi da kuma bukatun
cigaba a yankin.
Jakadun biyu sun
kuma ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijira da cibiyar sojojin Nijeriya da kuma
wasu ofisoshin ma’aikatan jinkai kafin ziyarar Gwamna Zulum.
Babban Jami’in
Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya Edward Kallon ya jagoranci tawagar jakadun
wadanda suka bayyana damuwa kan matsalar tsaron da ya addabi yankin da kuma
illar da ya yiwa kasashen dake Yankin tafkin Chadi da suka hada da Kamaru da
Nijar da kuma Chadi na sama da shekaru 10.
Majalisar Dinkin
Duniya tace tashin hankalin da aka kwashe sama da shekaru 10 ana yi ya yi
sanadin raba mutane sama da miliyan 3 da dubu 200 da matsugunan su, yayin da
kusan miliyan 4 da rabi ke fuskantar barazanar yunwa da kuma kuncin rayuwa.
Kallon yace a
arewa maso gabashin Najeriya kawai mutane sama da miliyan 13 ke zama a yankunan
da ake fama da tashin hankali, kuma daga cikin su miliyan 8 da dubu 700 na
bukatar agajin gaggawa.
0 Comments