Gwamnan Zamfara Ya Dakatar Da Sarkin Dansadau

 



Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da kuma Dagacin Nasarawa Mailayi, Bello Wakkala, saboda zarginsu da alaƙa da 'yan fashin daji.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Zailani Bappa ya fitar, dakatarwar ta fara aiki ne nan take.

Kazalika gwamnan ya umarci Dagacin Dansadau Nasiru Muhammad S/Kudu da ya karɓi ragamar masarautar nan take.

A gefe guda kuma, Bello Matawalle ya kafa wani kwamati da zai binciki ayyukan shugabannin da aka dakatar.

"'Yan kwamatin sun haɗa da DIG Mohammad Ibrahim Tsafe (mai ritaya) a matsayin shugaba, da Yusuf Alhassan Kanoma da Ibrahim T Tukur da Sheikh Ahmad Umar Kanoma da Sheikh Abdullahi Umar Dalla Dalla da Sheikh Kabir Umar Maru da Barista Abdurrashid Haruna a matsayin sakatare."

Jihar Zamfara ta yi ƙaurin suna wajen kashe-kashe da 'yan fashi ke aikatawa kusan kullum, yayin da gwamnatin jihar ke cewa shirinta na sasantawa da 'yan bindigar afuwa na taimakawa wajen raguwar hare-haren.


-BBC HAUSA

Post a Comment

0 Comments