Ma’aikatun Jihar Kaduna da dama daga shekara ta 2020 zuwa yau sun yi tsare-tsaren daukan aiki mutum 10,000 ciki har da ma’aikata...
Ma’aikatun Jihar Kaduna da dama daga shekara ta 2020 zuwa yau sun yi tsare-tsaren daukan aiki mutum 10,000 ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya da ma’aikatar ilimi.
Duk da yanayi na rashin tabbas da duniya ta samu kanta saboda bullar annobar Korona Bairos, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba ma’aikatu da hukumomin da suke samar da ayyuka masu muhimmanci damar daukan aiki domin su kara karfin ma’aikatunsu. Ganin irin muhimmancin ma’aikatar ilimi da ma’aikar kiwon lafiya sun cika ciki wurin daukan wannan aikin, da kuma alkawarin da gwamnati ta yi na bayar da ilimi kyauta daga matakin firamare zuwa sakandare. Yanzu haka Hukumar ta gudanar da intabiyu na daukar malaman sakandare 7,600.
Asibitin Koyarwa na Barau Dikko ta dauki ma’aikata 283 wadanda suka hada da likitoci da ma’akatan jinya a watan Nuwamba na 2020. Wanda hakan ya sa yawan likitocin da ke asibitin suka karu zuwa 191 koma bayan likitoci 32 da wannan gwamnatin ta sama a shekara ta 2015. A takaice yanzu yawan likitocin da ke karkashin Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna sun karu daga 2015 zuwa 406 wadanda yanzu haka suke aiki a asibitoci daban daban na gwamnati.
Bugu da kari, Ma’aikatar Lafiya ta dauki karin ma’aikatan kiwon lafiya 1,064 hade da ma’aikata masu kwarewa a fannoni daban daban guda 196 da kuma sauran ma’aikata 871. Yanzu haka ma’aikata 1,225 da aka dauka aiki an tura su zuwa cibiyoyin kiwon lafiya daban daban da ke jihar.
Sannan a matakin manyan makarantu na gaba da sakandare, daga shekara ta 2020 zuwa yau Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta dauki ma’akata 159. Kwalejin Ilimi na Gidan Waya da ke Kafanchan ta bayar da rahoton daukan sababbin ma’aikata 388 wanda suka hada da malamai da sauran fannoni wanda yanzu haka suna jiran amincewa domin wadannan ma’aikata su fara zuwa aiki.
A sauran fannoni kuwa, Hukumar Kula da Rarraba Ruwa ta dauki fiye da ma’aikata 14.
A karshe, a kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi na daidaita yawan ma’aikatanta, za ta ci gaba da daukan kwararrun ma’aikata a fannoni daban daban da ake da bukata. Sannan duk wani gibi da wannan kokarin daidata ma’aikata zai haifar, gwamnati za ta yi kokarin zakulo wasu daga cikin wadanda suka nemi gurbin aikin da aka dakatar a lokacin bullar annobar Korona Bairos domin su cike wancan gurbi da ake bukata.
Sa Hannu
Muyiwa Adekeye
Mai Ba Gwamna Shawara Kan Kafafen Yada Labarai
No comments