Gwamnatin Katsina Ta Gwangwaje 'Yan Kwallon Katsina United Da Sabuwar MotaGwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta saya ma kungiyar kwallon ƙafa ta Katsina United sabuwar mota kirar Coaster.

A jiya Laraba 16 ga watan Yunin 2021 Kwamishinan Matasa da wasanni na jihar Katsina Honorabul Sani Aliyu Danlami ne ya kaddamar da motar ga kungiyar a filin wasa na Muhammadu Dikko dake cikin garin Katsina.

Post a Comment

0 Comments