Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Twitter Na Neman Sasanci Da Ita


Ministan ƴada labarai da al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed ya ce hukumomin kamfanin Twitter sun tuntuɓi gwamnatin kasar domin tattaunawa kan matakin dakatar da amfani da shafin da gwamnatin Nijeriya ta yi.

Rahototanni sun bayyana cewa ministan ya shaida wa manema labarai hakan ne bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban ƙasa a ranar Laraba, inda ya ce kamfanin Twitter na neman “tattaunawa mai ƙarfi” don warware matsalar da ta kai ga dakatar da ayyukansa a Nijeriya.

“Shugabannin gudanarwar Twitter sun tuntuɓi gwamnati a ranar Laraba,” in ji Lai Mohammed.

A ranar juma’a gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da ayyukan Twitter kan zarginsa da bayar da dama ga waɗanda ke barazana ga ɗorewar Nijeriya.

Dakatarwar na zuwa bayan kamfanin ya goge ɗaya daga cikin sakonnin shugaban Nijeriya inda ya ke barazanar ɗaukar mataki kan masu da’awar ɓallewa daga Nijeriya.

An kuma ambato Lai Mohammed na cewa, dgaa yanzu duk wani kamfanin kafar sadarwa sai ya yi rijista tare da ba shi lasisi kafin ya fara ayyukansa a Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments