Gwamnatin Tarayya Ta Tsaurara Matakan Yaki Da Cutar Korona

 


Gwamnatin Tarayya ta tsawaita dokar hana baki daga kasashen Brazil da India da Turkiya shiga cikin kasar ta saboda dakile yaduwar cutar korona wadda tayi kamari a cikin kasashen su.

Gwamnatin kasar ta kuma sanya sunan Afirka ta Kudu cikin jerin kasashen dake nahiyar Afirka da dokar ta shafa bayan kasashen Zambia da Rwanda da Namibia da kuma Uganda.

Shugaban kwamitin yaki da cutar kuma Sakataren Gwamnati Boss Gida Mustapha ya sanar da sabon matakin inda ya kara da cewar sabuwar dokar za tayi aiki na makwanni 4 kafin sake nazari akan ta.

Mustapha yace suna sanya ido akan abubuwan dake faruwa a kasashen duniya dangane da abinda ya shafi cutar domin daukar matakan da suka dace na kare lafiyar Yan Najeriya.

Sakataren Gwamnatin ya baiwa Yan Najeriya shawarar ci gaba da sanya ido sosai da daukar matakan kare lafiyar su ganin yadda ake samun sake dawowar cutar a wasu kasashen Afirka.

Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewar suna mayar da hankali akan batun samar da maganin rigakafi wajen ganin an yiwa jama’ar kasar allurar domin kare kan su daga harbuwa da cutar.


Post a Comment

0 Comments