Harin Makarantar Kebbi: Sojoji Sun Kuɓutar Da Wasu Ɗaliban FGC Yawuri

 


Bayanan da ke fitowa daga jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa sojoji sun kuɓutar da wasu daga cikin yara 'yan makarantar Gwamnatin Tarayya ta garin Birnin Yawuri da aka sace.

Rahotannin sun ce sojojin sun yi wa ɓarayin ƙofar rago ne a ranar Alhamis da daddare a cikin daji.

Ɗan majalisa mai wakilar Yawuri a majalisar dokokin Kebbi Honorabul Muhammad Bello Ngaski ya tabbatar wa da BBC Hausa labarin.

A ranar Alhamis da rana ne ƴan bindigar suka kutsa makarantar tare da sace yaran.

Wasu shaidu sun shaida wa BBC cewa sun ga gawar ɓarayin dajin fiye da 80.

Shaidun sun ce an yi gumurzu sosai tsakanin dakarun tsaro da ɓarayin dajin a ƙaramar hukumar Sakaba ta jihar Kebbin.

Sun ƙara da da cewa sojojin sun katse wa ɓarayin hanzari ne ta hanyar yi musu kwanton ɓauna a hanyar tafiya da yaran da suka sata zuwa maɓoyarsu.

"Abin da ya faru a garin Makoko wanda su ɓarayin suka mai da daji, sojoji sun tare su suka yi artabu. Yanzu haka maganar da nake maka an tara gawa sama da mutum 80 na ɓarayin.

"Su kuma yaran yanzu haka akwai kusan bakwai da tabbas sun dawo an anso su. Sannan sojojin sun zagaye dajin da ɓarayin suke, don tun jiya aka tare musu hanyoyin don haka sun kasa gaba sun kasa baya," in ji wani ganau.

Akwai tazara sosai tsakanin wajen da lamarin ya faru da kuma birnin Yawuri da ak sace yaran.


Artabu

Ganau ɗin ya ƙara da cewa: "A yanzu haka dai yanar sun Makoko kuma tuni shugaban ƙaramar hukumar Sakaba ya tura likitoci su duba yaran."

A yanzu dai shaidu sun ce ana ci gaba da tara gawarwakin ɓarayin a wata makarantar firamare da ke garin Makokon, "sannan kuma ba mu ga gawar soja ko ɗaya ba," in ji shaidun.

Honorabul Ngaski ya ce tun a jiya aka sa jami'an tsaro su tare hanyar Sakaba inda nan ɓarayin ke bi . "Yanzu haka yara tara aka ƙwato daga hannunsu," in ji shi.

Ya ƙara da cewa yaran na cikin halin lafiya sai dai suna cikin ɗimuwa, "kuma ba a danƙa mana su a hannu ba. Mai girma gwamna dai na tare da mu yanzu haka na san sai daga baya za a ba mu su a hukumance."

Honorabul Ngaski ya ci gaba da cewa har zuwa yanzu ba su san yawan yaran da aka sace ba amma dai iyaye sun yi rijistar fiye da yara 50 da ba a gani ba.

"Muna sa ran dai wasu sun shiga daji ne ba a gansu ba," a cewarsa.

Masu sharhi na ganin wannan nasara a matsayin wani lamari da jami'an tsaron Najeriya suka fara gano bakin zaren satar jama'a.

Kuma ana ganin idan har suka ci gaba da ɗabbaka irin wannan dabarar yaƙin to batun satar mutane a shiga daji da su ka iya zuwa ƙarshe.

Post a Comment

0 Comments