Iraki da Masar da Jordan sun amince suyi aiki tareKasashen Masar da Jordan da Iraki sun amince da batun daukaka hadin kai ta fannin tsaro da tattalin arziki a tsakaninsu, yayin wata ziyara da shugaban Masar ya kai Iraki a karon farko cikin shekaru 30.


Rfi Hausa ta labarto cewa wannan ziyarar da shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi da sarkin Abdallah na 2 na Jordan suka kai birnin Bagadaza na zuwa ne a daidai lokacin da Iraki ke kokarin matsowa kusa da kasashen Larabawa, kawayen Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Zalika Iraki na neman karfafa kanta a matsayin mai shiga tsakani a tsakanin kasashen Larabawa da Iran, bayan da aka ruwaito cewa ta karbi bakoncin tattaunawa tsakanin Iran da Saudiyya.

Sisi da Abdallah sun gana da shugaba Barham Saleh da Firaminista Mustafa al-Kadhemi, inda ma Saleh yake cewa haduwar tasu wani sako ne mai karfi ga duniya, a cikin yanayin da yankinsu ke fama da kalubale.

Taron tsakanin Kadhemi da bakin nasa ya tattauna batutuwa da suka shafi yankinsu, gami da laluben hanyoyin yaukka hadin kai  tsakanin Iraki, Jordan da Masar a fannin tsaro, makamashi da kasuwanci, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa a bayan taron.

Sun kuma tattauna batun bijiro da masalaha a rikicin Syria da ya shekara 10, daidai da manufofin majalisar dinkin duniya.

Post a Comment

0 Comments