Iran Ta Mallaki Jiragen Dake Cin Dogon Zango, Inji Shugaban Rundunar Soji Janar Salami

Rundunar zaratan sojin Iran ta ‘Revolutionary Guard’ ta ce ta mallaki jiragen sama masu sarrafa kan su da kan iya tafiya mai nisar kilomita 7,000.

Shugaban rundunar sojin kasar Janar Hossein Salami ya bayyana haka a jawabin da yayi ta kafar talabijin din kasar inda yake cewa irin wadannan jirage dake yawo ba tare da matuka ba kan je su sauka a inda aka bukace su.

Janar Salami bai yi cikakken bayani kan jiragen ba amma sanarwar ta sa na nuna cigaban da aka samu wajen kera irin wadannan jirage musamman irin sa da aka yiwa suna Gaza wadda ke tafiyar kilomita 2,000.

Kasar Iran na fama da matsalar mallakar sabbin jiragen saman soji sakamakon takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar kuma yanzu haka jiragen yakin da ta mallaka na daga cikin wadanda kasar ta saya ne a shekarar 1979 lokacin mulkin Sarki Shah.


Wannan ya sa kasar ta dogara da kera jiragen sama mau sarrafa kan su kamar wadanda akayi amfani da su wajen kai hare hare akan Yan tawayen Kurdawan dake iyakar kasar Iraqi.

A wannan wata aka zabi Ebrahim Raisi a matsayin sabon shugaban kasa domin maye gurbin Hassan Rouhani, kuma rahotanni sun ce shima yana da tsatsauran ra'ayi kamar shugaban addinin kasar Ayatollah Ali Khamenei.

Khamenei dake jagorancin kasar a matsayin shugaban addini tun bayan mutuwar Ayatollah Ruhollah Khomeinei a shekarar 1979 ke da karfin fada aji kan duk wasu batutuwan da suka shafi harkokin diflomasiyar kasar.

Post a Comment

0 Comments