Jami'ar Kimiyyah Ta Kano Za Ta Kulla Alakar Aiki Da Jami'ar MAAUN Domin Bunkasa IlimiShugaban Jami'ar Kimiyyah ta jihar Kano dake Wudil, Farfesa Shehu Alhaji Musa ya tabbatar da cewa Jami'arsa ta KUT dake Wudil za ta hada hannu da Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano domin bunkasa bangaren ilimi. 

Shugaban Jami'ar ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci tawagarsa ya kai ziyara zuwa ginin Jami'ar ta MAAUN dake titin Adamu Abubakar Gwarzo Road dake Hotoro GRA a Kano.

Farfesa Shehu Alhaji Musa ya yi matukar bayyana farin cikinsa bisa yadda ya ga aikin ginin Jami'ar da kuma kayayyakin zamani da aka zuba wanda ya hada da dakunan gwaje-gwaje, ajujuwan karatu, kayayyakin zamani a kowanne sashe, wuraren zama da sauransu daidai da ci gaban zamani. 


"Mun zo nan ne domin kawo ziyara ga Jami'ar MAAUN; a matsayina, na kasance abokin hulda wajen kafa Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, ina matukar farin cikin kasancewa da shugaba wajen ganin tabbatuwar wannan gagarumin aiki", inji shi. 


Farfesa Shehu ya ci gaba da cewa; "muna fatan  zamu duba hanyar kulla alaka a tsakanin Jami'o'in biyu. Muna sane da gudummawa da kuma sadaukarwar da shugaban Jami'ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo yake yi, muna son karfafa shi akan hakan muna kuma fatan zai dore", ya lurantar. 


Tunda fari sai da shugaban Jami'ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya jagoranci tawagar Jami'ar ta KUT din a karkashin Farfesa Shehu Alhaji Musa inda ya zagaya da su cikin Jami'ar ta MAAUN dake Hotoro GRA Kano, inda ya tabbatar musu da cewa bada jimawa ba Jami'ar za ta fara aiki a Kano. 

Ya kuma nuna jindadinsa bisa ziyarar da shugaban Jami'ar KUT din da tawagarsa ta kawo musu. Inda ya ce Jami'o'in biyu za su hada hannu wajen aiki tare domin bunkasa bangaren ilimi. 

Post a Comment

0 Comments