Jami’ar MAAUN Ta Taya Dalibanta Murnar Nasarar Cin Jarabawar Aikin Jinya Da Suka Yi A Nijeriya

 


Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) dake jamhuriyyar kasar Nijer ta taya dalibanta da suka fito daga Nijeriya murnar cin jarabawar kwararru da suka yi ta 2021 wanda Nijeriya ke shiryawa daliban da suka karanci bangaren aikin jinya da unguwanzoma (Nursing and Midwifery Council of Nigeria (NMCN)). 

Hukumar shirya jarabawar ma’aikatan jinyar da unguwanzoma ta Nijeriya, ta saki jarabawar kwararrun ne a ranar Laraba 23 ga watan Yunin 2021. 

Taya murnar ya zo ne a cikin takardar taya murnar da shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya aiko daga birnin Paris, kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Alhamis. 

A cikin sanarwar, Farfesa Abubakar Gwarzo ya bayyana jindadinsa bisa wannan nasarar da dalibansa suka samu, inda ya ce daliban sun sanya shi da jami’ar alfahari.

 “shugaba kuma mu’assasin Jami’ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo yana matukar farin ciki da daliban nan bisa kwazon da suka nuna domin sun sanya Jami’ar alfahari a duniya. Muna yi musu addu’ar samun nasara a dukkanin abin da suka sanya gaba a kuma duk inda za su samu kawukansu”, inji sanarwar. 

Farfesa Gwarzo har wala yau ya karfafi daliban da su ci gaba da nuna jajircewa tare da zama jakadu nagari ga Jami’ar. Sannan har wala yau ya taya iyaye da ‘yan’uwan daliban murna bisa nasarar da suka samu na cin jarabawar kwararrun ta NMCN. 

A karshe ya yi wa daliban addu’ar samun aiki a lokacin da ya kamata, inda ya bukaci da su yi aiki bisa dokoki da ka’idodin ayyukansu a duk inda suka sami kawukansu.  


Post a Comment

0 Comments