Jami'ar Maryam Abacha Ta Taya Alhaji Bachirou Ousmane Halal Murnar Cika Shekaru 49 A DuniyaHukumar Gudanarwa na Jami'ariar Maryam Abacha American University dake kasar Jamhuriyyar Nijer na taya shugaban gidan siyar da Abinci na 'HALAL  RESTURANT' dake cikin garin Maradi ta jihar Maradi dake Jamhuriyyar Nijer murna da farin cikin zagayowar ranar haihuwarsa a yau Laraba 2 ga watan Yunin 2021. 

Alhaji Bachirou Halal an haife shi ne a cikin garin Maradi a shekarar 1972. Kuma ya kasance mutum ne nagari, sannan abokin harkar yau da kullum ne na Jami'ar ta MAAUN ta bangaren kasuwancin siyar ma da Malamai da daliban Jami'ar abinci.  

"Don haka hukumar gudanarwa na Jami'ar ta Maryam Abacha American University dake Nijer na mika sakon ta ya murna ga Alhaji Bachirou Ousmane Halal. Da fatan Allah ya karo shekaru masu albarka da lafiya da imani da nisan kwana da karuwar arziki", inji sanarwar da Aliyu Yusuf Kakaki, Babban Sakataren Yada Labarai na Jami'ar Maryam Abacha American University ya fitar a yau Laraba 2 ga watan Yunin 2021. 

Post a Comment

0 Comments