Hukumar gudanar da jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) ta jajantawa gwamnati da dukkanin al’ummar kasar Zambia bisa rasuwa...
Hukumar gudanar da jami’ar Maryam Abacha American
University (MAAUN) ta jajantawa gwamnati da dukkanin al’ummar kasar Zambia bisa
rasuwar shugaban kasar na farko, Dr Kenneth David Kaunda, wanda ya mutu yana da
shekara 97 na duniya.
Kauda ya mutu ne a asibitin sojoji dake Lusaka a
ranar Alhamis din 17 ga watan Yuni bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Sakon jajen na dauke ne da sa hannun shugaban Jami’ar
kuma mu’assasin jami’ar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a takardar da ya rabawa
manema labarai a Kano a ranar Asabar.
A cewar sanarwar, mutuwar Kauda babban rashi ne ga
al’ummar Afrika da kuma kasar ta Zambia duba da yadda suka rasa dan kishin kasa
kuma jajirtacce wanda ya bayar da gudummawa da dama wajen ci gaban kasar sa.
"shugaba Kaunda shi ne shugaban kasar Zambia na
farko kuma babban jigo ne wajen fafutikar samar da ‘yancin kasar wanda
gudummawarsa wajen ci gaban kasar ya fi karfin a misalta”, inji sanarwar.
"Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American
University na Nijeriya, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a madadin hukumar gudanar
da jami’ar muna mika sakon jajenmu ga iyalan Marigayin, da kuma al’ummar Zambia
bisa rashin Dr Kenneth Kauda," sanarwar ta jaddada.
A karshe Farfesa Abubakar Gwarzo ya yi addu’ar ci
gaba da samun zaman lafiya, hadin kai da kuma daidaito tare da bunkasar tattali
arziki da ci gaba mai amfani ga al’ummar Zambia da ma nahiyar Afrika baki daya.
No comments