Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

KWANAKI 2000 NA TSARE SHAIKH ZAKZAKY: Almajiransa Sun Nemi Jama’a Su Fito Kwansu Da Kwarkwatarsu Su Yi Kururuwar Adalci

  Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun nemi al’umma baki daya da su fito su yi kururuwar adalci a daidai lokacin da jagoransu ke cika kwana...

 



Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun nemi al’umma baki daya da su fito su yi kururuwar adalci a daidai lokacin da jagoransu ke cika kwanaki 2000 gwamnatin Nijeriya na ci gaba da yi masa ‘haramtacciyar tsarewa’ duk da umurnin kotun kasa ta sake shi ta kuma biya shi diyyar take masa hakki da aka yi da matarsa. 

Almajiran na shi sun bayyana hakan ne a cikin sanarwar da suka raba a yau Alhamis, kuma Shaikh Abdulhameed Bello ya sanyawa hannu. 

Ga cikakken sanarwar kamar yadda MADOGARA ta samu kwafi; 

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Yau ake cika kwanaki dubu biyu (2000) na tsare Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky bisa zalunci. Mun fara ne da istirja’i a rubutun nan saboda Manzon Allah (S) ya umurci muminai da su yi haka in bala’i ya same su ko kuma sun tuna da masifa. Kuma tabbas hakika, zaluncin da ake ci gaba da yi wa Jagoranmu, Shaikh Zakzaky, babban masifa ne ga kasa baki daya, kuma muna ganin yadda sakamakon zaluncin ke bibiyan wannan kasar tun hawan wannan gwamnatin ta Buhari.

Tun bayan auka wa Shaikh Zakzaky da almajiransa a Disamban 2015 da sojoji suka yi, inda suka kashe mutane sama da dubu da lalata dukiya ta miliyoyin Nairori da jikkata daruruwan jama’ar da ba su da makami, gwamnatin nan ta jiha ta Elrufa’i da ta gwamnatin Tarayya ta Buhari suka rika zarge-zarge marasa tushe kan Shaikh Zakzaky da Harkar Musulunci a kafafen yada labarai, maimakon a kotu, a kokarinsu na gamsar da jama’a cewa abin da suka yi ya yi daidai.

Sai dai kash! Kwanaki dubu biyu yanzu bayan nan duk zarge-zargen da suka yi wa Shaikh Zakzaky da almajiransa ta bayyana wa duniya cewa, sun fake ne da guzuma don su harbi karsana. Alal misali sun yi ta ihun cewa wai an tare wa Janar Buratai hanya ne shi ya sa sojoji suka yi kisan kiyashi a Zariya. Sai ga shi jama’a kowa na gani ‘yan bindigan daji suna tare hanyoyi mota na manyan titunan kasar nan, kuma gwamnati ta kasa yin komai a kai. Jama’a shaidu ne na yadda ‘yan A-waren Iyamurai da Yarbawa suke tare hanyoyi, su ce kar a wuce, kuma a ki wucewan, amma gwamnati ta kasa yin komai a kai. To, me ya sa sai a kan Shaikh Zakzaky da jama’arsa za a nace kan zargin da ma ba shi da tushe balle makama, wai ana tare hanya?

Har ila yau wannan gwamnatin da ‘yan kanzaginta sun sha zargin cewa wai Jagoranmu da almajiransa sun kafa gwamnati cikin gwamnati, don dai su nuna kisan yara da mata da suka yi a Zariya daidai ne. Sai ga shi jama’a suna ji suna gani, ‘yan bindigan daji sun wafci garuruwa da kauyuka a kusan duk jihohin Arewacin kasar nan, sun hana jama’a da jami’an tsaro damar walwala a cikin su. Kuma gwamnati ta kasa tabuka komai don ganin ta hana hakan. Me ya sa sai Shaikh Zakzaky da jama’arsa za a yi wa wannan zargi wanda shi ma mara tushe ne? In dai ana neman wadanda suka kafa gwamnati ne cikin gwamnati, to ai ‘yan A-waren Iyamurai da Yarbawa  da ‘yan bindigan daji su ne abin tuhuma a kai, amma ba Shaikh Zakzaky da Harkar Musulunci ba.

Sannan kuma da yake sun iya kage da sharri suka ce, Shaikh Zakzaky da Harkar Musulunci suna da muggan makamai. Sai Allah ya tona musu asiri, yanzu jama’a kowa ya san kungiyoyin da ke rike da makamai irin su ‘yan A-waren Iyamurai da Yarbawa da ‘yan Bindigan daji da suka addabi Arewacin kasar nan. Kuma gwamnati ta kasa yi musu komai. Don haka babu wani dalili na tsangwamar Shaikh Zakzaky da jama’arsa kan wannan zargi mara tushe balle makama.

Karshe ma dai uwargijiyar gwamnatin nan, wato gwamnatin kasar Amurka ta shelanta wa duniya cewa Shaikh Zakzaky fursunan siyasa ne. Ma’ana ana tsare da shi ne kawai saboda fahimtarsa ta addinin Musulunci. Abin da Amurka take nufi shi ne ana tsare da shi ne ba don ya aikata wani laifi ba. Tunda ko har Amurka za ta iya fadidn haka, duk da irin adawar da take nuna wa kasashen Musulunci, to lalle ba karamin zalunci ta ga an yi wa Jagoranmu ba, har ya sa ta fadi hakan.

Don haka muna kara kira ga jama’an kasar nan da su fito kwansu da kwarkwatarsu don goyon bayan adalci, wanda shi ne ganin cewa an saki wannan Jagora namu wanda bai tare wa kowa hanya ba, bai kashe kowa ba, kuma bai dauki makamai ba a gwagwarmayar da yake yi na ganin tabbatar addinin Allah a bayan kasa. Kin shiga wannan gwagwarmayar tamkar yarda da zaluncin da aka yi masa da jama’arsa ne a Disamban 2015 a Zariya, wanda kuma yarda da hakan tamkar jawo wa al’umma fushin Allah ne, wanda kuma ga shi nan jama’a kowa na dandana kudarsa ta hanyoyi da dama.

Su kuwa azzaluman gwamnatocin kasar nan muna kira gare su da su yi wa kansu kiyamullaili, su saki Jagoranmu Shaikh Zakzaky da sauran wadanda suke tsare da su ba tare da wani bata lokaci ba. Har zuwa yaushe za su saki Malamin da suka shafe shekaru shida suna zalunta? Wannan zaluncin ya isa haka nan! A sake shi ko Allah ya tausaya wa al’ummar kasar nan.

SA HANNU:

SHAIKH ABDULHAMID BELLO, ZARIA

03/06/2021


No comments