Daga Yahaya M Abdullahi
Taron Kungiyoyin Arewa da suka hada da Northern Consensus Movement, da sauransu sun saka kimanin zunzurutun kudi har naira miliyan Dari Ga dukkan wanda ya kawo shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu a mace ko a raye.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a ranar Alhamis a birnin Tarayya dake Abuja.
Kungiyar ta ce Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da daman gaske daga sassan jihohin arewacin Nijeriya dama Kudancinta, saboda haka kama shi da gurfanar da shi ya zama wajibi a cewarsu.
0 Comments