Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Ta Taya Farfesa Killion Munyama Murnar Samun Mukamin Jami'in Diflomasiyya A Kasar Poland

Shugaba kuma mu'assasin Jami'ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya Farfesa...Shugaba kuma mu'assasin Jami'ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya Farfesa Killion Munzele Munyama murnar mukamin da aka bashi a matsayin jami'in Diflomasiyya a  Tarayyar Turai. 

Munyama, wanda ya kasance dan Afrika kwallon kwal a matsayin memba a majalisar Poland ya bar majalisar kasar domin karbar mukamin da aka ba shi a matsayin jami'in Diflomadiyya ta Tarayyar Turai da zai rika hulda da nahiyar Afrika.


Takardar taya murnar na dauke ne da sa hannun, shugaban MAAUN, Farfesa Abubakar Gwarzo wanda ya aiko daga birnin Paris kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin. 


A cewar Farfesa Gwarzo, Munyama ya cancanci mukamin da aka ba shi idan aka yi duba da kwazonsa da kwarewar da yake da shi a matsayinsa na Malamin Jami'a kuma dan siyasa wanda ya kwashe shekara 10 a matsayin memba a majalisar kasar Poland daga shekarar 2011 har zuwa 2021. 
 

"Gami da karawa kan aikinsa a majalisar, Munyama yana aiki a matsayin memba a tawagar Italiya ga majalisar hukumar Turai (PACE) tun 2015", inji Farfesa Gwarzo. 


Farfesa Gwarzo ya ci gaba da cewa; "yana daga cikin jam'iyyar mutanen Turai wato 'the European People's Party group', kuma memba ne a kwamitin masu lura da masu gudun hijira, da wadanda yaki ya jigata wato 'Committee on Migration, Refugees and Displaced Persons', tun shekarar 2015. Kuma yana karkashin kwamitin hulda da kasashen waje don samun hadin kai (tun shekarar 2020). Kuma shi ne shugaban PACE dake lura da tsare-tsaren kasashen ketare", ya tabbatar. 

Ya kara da cewa; "ya kasance marubuci a majalisar akan sha'anin jinkai da kare hakkin 'yan gudun hijira a Turai a 2018. Daga 2015 har zuwa 2017, ya kuma rike mukami a karkashin kwamitin dake lura da dunkulewa". 


Ya ajiye mukaminsa a majalisar kasar Poland ne a ranar 10 ga watan Yunin 2021 bayan da ya amince da zai yi aiki da ma'aikatar Turai din (European External Action Service). 


"A don haka, a madadin kaina da iyalina da kuma hukumar gudanar da jami'ar MAAUN, ina taya ka murnar mukamin da ka samu a ma'aikatar Diflomasiyya ta Tarayyar Turai", inji Farfesa Abubakar Gwarzo. 


A karshe ya yi addu'ar Allah ta'ala ya taimaki Farfesa Munyama wajen sauke nauyin da ya rataya a kan shi bisa sabon aikin da aka ba shi ya yi aiki da ma'aikatar Diflomasiyya ta Tarayyar Turai wajen hulda da nahiyar Afrika.

No comments