Mahaifin Mawallafin Jaridar SolaceBase, Sarkin Ilorin Abubakar Jos Ya Rasu


Balogun Alanamu na Ilorin, Alhaji Abubakar Akanbi Jos ya rasu.

Alhaji Abubakar Jos, mahaifin mawallafin Jaridar Solacebase.com, Abdullateef Abubakar Jos, ya rasu a yau Juma’a.

Mai martaba Sarki Balogun Alanamu na 11 ya rasu yana da shekara 96 kamar yadda Jaridar Alkiblah ta labarto.

An yi sallar jana’izarsa da misalin karfe 4.00 na Yamma a harabar Balogun Alanamu a yau Juma’a.

Abubakar Jos ya rasu ya bar mata biyu, da yara da yawa, da jikoki da ƴaƴan jikoki.

Post a Comment

0 Comments