Mahara Sun Kashe Dan Majalisar Jihar ZamfaraDaren jiya 'yan ta'adda sun kashe dan Majalisa mai wakiltar Shinkafi a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.

Dan Majalisar ya mutu a wani hari da suka kai masa da dansa da direbansa a tsakanin Kankara ta Jihar Katsina da Zamfara.

Dan Majalisar Muhammad G. Ahmad na kan hanyarsa ne ta zuwa Kano don zuwa filin jirgi da nufin yin tafiya kasar waje.

Madogara: The Links News

Post a Comment

0 Comments