Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Dinkin Duniya Ta Gaza Amincewa Da Kasafin Kudin Samar Da Zaman Lafiya

  Kasashe 193 dake Majalisar Dinkin Duniya sun gaza cimma matsaya domin amincewa da kasafin kudin gudanar da aikin samar da zaman lafiya da ...

 


Kasashe 193 dake Majalisar Dinkin Duniya sun gaza cimma matsaya domin amincewa da kasafin kudin gudanar da aikin samar da zaman lafiya da ake saran fara aiki da shi daga ranar 1 ga watan Yuli mai kamawa matakin da ake ganin zai dakatar da ayyukan dakarun a kasashe da dama.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar gazawar ta biyo bayan wasu karin bukatu da kasar China da wasu kasashen Afirka suka sake gabatarwa Majalisar wadanda zasu shafi kudaden da ta ke da su wajen gudanar da ayyukan ta na yau da kullum.

Majalisar Dinkin Duniya na da kasafin Dala biliyan 6 da rabi kowacce shekara domin gudanar da aikin samar da zaman lafiyar daga ranar 1 ga watan Yulin kowacce shekara zuwa 30 ga watan Yunin shekara ta gaba.

Mai Magana da yawun Majalisar Stephane Dujarric yace Majalisar za tayi wani tanadi har zuwa lokacin da kasashen dake cikin ta zasu amince da kasafin da ake bukata.

Dujarric yace bisa ka’ida Sakatare Janar na da hurumin samar da kudaden da za’ayi amfani da su wajen kare lafiyar ma’aikata da dakarun Majalisar har zuwa lokacin da za’a amince da kasafin, yayin da dakatar da aikin zai shafi aiwatar da muradun Majalisar da suka hada da tallafin yaki da annobar korona da kare fararen hula.


No comments