Manhajar Crowwe Ta Nada Sabon Mai Gudanarwa A Harshen Hausa


Daga Aliyu Adamu Tsiga 

Gloomme Business Collection Limited, mai kamfanin Crowwe  Adamu Garba ll, ya nada Auwalu Nakarkata Dambatta a matsayin Kodinetan Shirin Media na sashen Hausa.

Babban jami'in kamfanin Anya Afunaya, ne ya tabbatar da hakan a cikin takardar nadin da ya sanya wa hannu a ranar Talata.

"Wannan wasikar ita ce don tabbatar da kai a matsayin mai kula da shirin  Media na Crowwe, cikin harshen Hausa don shirye-shiryen Media  da za a shirya;  aikin ka shi ne tabbatar da cewa an hada su yadda ya kamata don tabbatar da nasara wajen tallata wannan manhaja,” kamar yadda Afunaya ya rubuta a cikin wasikar.

Yayin gabatar da wasikar nadin, Adamu Garba ya kira Auwal Dambatta a matsayin mutum mai kwazo wanda ke nuna kwazo a koda yaushe don samun nasarar duk abin da yake yi.

Ya kuma bukaci wanda aka nada ya yi aiki ba tare da gajiyawa ba wajen tallata manhajar sannan ya ce babban kalubale ne ga Dambatta kasancewar harshen Hausa yare ne da ake magana da shi a Yankin Saharar Afirka.  “Ina mai karfafa maka gwiwa ta yadda za ka iya isar da shi da kyau Auwalu” in ji Adamu Garba ll.

A na shi bangaren, Auwalu Dambatta ya gode wa Adamu Garba ll, saboda yadda ya same shi da cancantar nada shi a matsayin daya daga cikin Manajan Kamfanin ya kuma yi alkawarin sadaukar da kansa wajen bunkasa Crowwe ba kawai a Afirka ba har ma da duniya baki daya.

Auwalu Nakarkata Dambatta shi ne Babban Darakta a Fitila Multi Media Ventures, ya yi aiki tare da gidajen rediyo daban-daban a Kano kuma ya buga labarai da yawa a cikin Harshen Hausa da Turanci.

Post a Comment

0 Comments