Masu Zanga-zanga Sun Hana Shiga Da Fita Birnin Gusau Na Zamfara


Wasu fusatattu mazauna garin Bungudu da kewaye da ke Jihar Zamfara sun toshe babbar hanyar shiga birnin Gusau da zummar nuna ɓacin ransu game da hare-haren 'yan fashin daji da suka addabe su.

Mutanen garin waɗanda mafi yawansu mata ne da yara sun tare hanyar ce da safiyar Juma'a, inda suka haddasa cunkoson ababen hawa.

Zanga-zangar tasu ta sa babu mai iya shiga ko fita daga Gusau, babban birnin Jihar ta Zamfara.

Masu zanga-zangar sun shaida wa BBC cewa sun fito ne bisa tsoron hare-haren 'yan bindiga bayan sojojin da ke bai wa garinsu tsaro sun sun fice daga garin.

Mutumin wanda muka ɓoye sunansa ya ce 'yan bindigar sun kashe soja ɗaya da ɗan sanda ɗaya a harin da suka kai kasuwar Bingi sannan suka ƙone ta ƙurmus tare da ɗibar kayayyakin mutane.

Ya ce mutanen sun yi tafiyar kusan kilomita 30 tare da kayayyakinsu kafin su fito bakin babban titin.

Hukumomin tsaro a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin amma mai magana da yawun rundunar soja a jihar ta Zamfara Kyaftin Yahaya Arama ya faɗa wa BBC cewa ba janye sojojin aka yi ba kwatakwata.

Ya ce an mayar da su ne domin sake tura wasu da za su maye gurbinsu har ma da kari, kuma yanzu haka a cewarsa tawaga-tawaga ta sojojin na kan hanyar zuwa yankin.

Ranar Asabar da ta wuce mazauna garin Gonin Gora da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna suka tare hanyar don nuna fushinsu game da hare-haren 'yan fashi, inda suka tsayar da zirga-zirgar matafiya ta fiye da awa biyar.


-Bbc Hausa

Post a Comment

0 Comments