Matasa Masu Zafin Kai Da Suke Kada Gangar Yaki Ba Su San Yaki Ba -Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa shugabannin rundunonin tsaron kasar umarnin murkushe masu tunzira tashin hankali da kuma kona kadarorin gwamnati domin biyan bukatar kan su.


Buhari wanda ya ce ya na samun rahotannin abin da ke faruwa a fadin kasar kowacce rana, ya ce fatar wadannan mutane ita ce ganin wannan gwamnatin ta gaza, ganin yadda batun rashin tsaro a Nijeria a yau ya zama abin magana a fadin duniya.

Shugaban ya bayyana damuwa akan yadda kokawar neman mulki ya koma hanyar lalata kasa, inda ya kara da cewa hakurin su ya kare dangane da irin wannan mutane.

Buhari ya sha alwashin ci gaba da mulkin Nijeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, saboda nauyin da 'yan Nijeriya suka dora masa bayan ya zagaya Jihohi 36 wajen neman goyan bayan su.


Shugaban ya ce wasu da ke nuna rashin hankali a wani yanki na Nijeriya ba su da yawan shekarun da za su fahimci irin halin da aka shiga da kuma asarar rayukan da aka yi lokacin yakin basasa, yayin da ya ke cewa su da suka je fagen daga lokacin suka kuma gwabza yaki za su fahimtar da su ta hanyar da za su gane nan bada dadewa ba.

Muhammadu Buhari ya ce ya sauya shugabannin manyan hafsoshin sojin kasar tare da Sufeto Janar na 'yan sanda kuma ana bukatar su sauke nauyin da aka dora musu.

Dangane da kona ofisoshin hukumar zabe kuma, shugaban ya ce zai bai wa INEC duk abin da ta ke bukata domin gudanar da ayyukanta.

Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hare-hare sau 42 aka kaiwa ofisoshin ta a Jihohi 14 abin da ke barazana ga shirin zabe mai zuwa.

Post a Comment

0 Comments