Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsalar Kasarnan 'Yan Nijeriya Ne, Inji Shugaba Buhari

  Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya ce ba bambancin addini ko ƙabilanci ne matsalar ƙasar ba, mutanen ƙasar ne matsalarta. Ya faɗi hak...

 


Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya ce ba bambancin addini ko ƙabilanci ne matsalar ƙasar ba, mutanen ƙasar ne matsalarta.

Ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin ƴan ƙungiyar Muhammadu Buhari/Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group, da ke goyon bayan shugaban da mataimakinsa, a ranar Laraba.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, Buhari ya ce "kanmu za mu zarga idan aka zo batun halin da Najeriya ke ciki, saboda irin rashin adalcinmu."

Sanarwar ta ce ƴan ƙungiyar sun kai wa Buhari ziyara ne don gabatar masa da kundin irin nasarorin da aka samu a tsawon shekara biyar na mulkinsa.

A yayin da shugaban ke ganawa da ƴan ƙungiyar, ya yi waiwaye kan irin fadi tashin da ya shafe shekaru yana yi don ganin an yi masa adalci a zaɓukan da yake da yaƙinin ya yi nasara a cikinsu.

Ya bayar da misali da cewa a zaɓukan 2003 da 2007 da kuma na 2011, duk mutanen da suka ƙi yi masa adalci ƴan ƙabilarsa ne kuma addininsu ɗaya.

Yayin da waɗanda suka tsaya masa kai da fata kuma suka kasance ƴan wata ƙabilar daban kuma addininsu ba ɗaya da shi ba.

"Matsalarmu ba ƙabilanci ko addini ba ne, mu ne matsalar kanmu," in ji shugaban.

'Yadda Hausawa ƴan uwana suka danne min haƙƙi a kotu'

"Bayan halarta ta uku a gaban Kotun Ƙoli, na fito na yi magana ga wadanda suke wajen a lokacin. Na ce musu daga wannan shekara ta 2003, zan yi wata 30 ina zuwa kotu.

"Shugaba Kotun Ƙolin wanda ya saurari ƙarar takarancin shugabancin ƙasar a lokacin, ajinmu ɗaya da shi a makarantar sakandare a Katsina. Mun shafe shekara shida a aji ɗaya tare da Mai Shari'a Umaru Abdullahi.

"Shugaban lauyoyina shi ne Cif Mike Ahamba, kirista kuma ɗan ƙabilar Ibo. A lokacin da babban alƙalin kotun ya buƙaci mu gabatar da ƙararmu, shaidana na farko ya bayyana.

"Ahamba ya dage sai an aika wasiƙa ga hukumar zaɓe ta INEC, don ta gabatar da rijistar mazaɓun wasu jihohin, don tabbatar da cewa abin da suka sanar ƙarya ne. Tsarawa aka yi.

"A yayin da suka yanke hukunci, wani mutumin daban ɗan ƙabilar Ibo marigayi Mai Shari'a Nsofor, ya nemi jin ta bakin INEC kan wasiƙar da aka aika masa.

"Sai suka yi watsi da ita. Daga nan sai ya yanke hukuncin da ya saɓa na sauran alƙalan. Wannan fa bayan shafe wata 27 kenan ana zuwa kotu.

"Mun tafi Kotun Ƙoli. Wane ne babban mai shari'ar a lokacin? Bahaushe ne Bafulatani ɗan uwana, da ya fito daga Zariya.

"Mambobin tawagar sun shiga ciki sun yi kamar minti 30, sannan suka fito hutun gajeren lokacin. Da suka koma ba su fi minti 15 ba suka kori ƙarar.

"A shekara 2007, wane ne babban mai shari'ar? Kutigi ne. Shi ma Musulmi ne daga arewacin Najeriya. Bayan wata takwas ya kori ƙarar.

"Haka ma a 2011, saboda dagewa ta, Musdafa, wani Bafulatani kamar ni, ɗan Jigawa, shi ne babban mai shari'ar. Ya kori ƙara ta.

Babu Mai Zargina Da Cin Hanci

"Na ba ku wannan labarin ne don ya tabbatar muku da cewa matsalarmu ba ta ƙabilanci ko bambancin addini ba ce. Mu ne matsalar kawunanmu.

"Na ƙi yarda na bayar da kai. Na yi ƙoƙarin komawa farar hula bayan abin da ya faru da ni a soji. An min abin da na yi wa waɗansu. Kun sani.

"A ƙarshe ni ma an kamani, aka ɗaure ni, amma an musu abin da suka yi. Na shafe shekara uku da ƴan kai. Haka Najeriya take.

"Ina fata malaman tarihi da masana za su adana wannan, don kuwa wani ci gaba ne mai kyau a siyasance.

"Ya kamata jikokinmu da tattaɓa-kunninmu su san fafutukar da aka yi. Ba mu samu komai da sauƙi kamar yadda mutane suke tunani ba.

"Ba wai don ɗumbin ma'adinan da yawan mutanen da muke da su ba. Mun sha wahala sosai a wannan tafiyar.

"Na yi ƙoƙarin fadar waɗannan abubuwa ne don ku haɗa kanku, ku yi amfani da albarkatunku, da ƙarfinku ba tare da na saka hannu ba.

A ƙarshe Shugaba Buhari ya yaba wa mambobin ƙungiyar tare da gode musu a kan soyayyar da ya ce suna gwada masa.

"Ba ni da bakin gode muku. Na gode muku sosai da sauran ƴan Najeriya saboda a 2019, na ziyarci dukkan jihohi, (saboda na sadaukar da kaina don bauta wa Najeriya da ƴan Najeriya, soyayya ce mara algus.)

"Na gode Allah ganin cewa cikin tsawon shekarun nan ba za su zarge ni da cin hanci ba.

"Kuma na yi abubuwa da yawa a rayuwata daga gwamna zuwa Ministan Man Fetur da shugaban ƙasar mulkin soji da kuma shugaban kasar farar hula har karo biyu.

"Na gode muku da ganin babu wanda ya tilasta ku, amma kuka hada kanku, kuka yi amfani da ƙarfinku da lokacinku, na gode muku sosai. Ina tabbatar muku da cewa, tarihi zai yi muku adalci.

 

Daga BBC Hausa

No comments