Daga Aqil Abdulkadir A yau Alhamis 17 ga watan Yunin 2021, aka shiga rana ta biyu da Malaman Kusfa a Zariya suka kira gangami do...
Daga Aqil Abdulkadir
A yau Alhamis 17 ga watan Yunin 2021, aka shiga rana ta biyu da Malaman Kusfa a Zariya suka kira gangami domin yin Alkunuti saboda yadda masu satar mutane suka addabi garin na Zariya.
A yau ma an gabatar da sallah raka'a 2, inda bayan kammalawa aka yi addu'a.
A yau wanda ya jagoranci sallar ya fito ne daga gidan Malam Na'iya.
Shehu Amal (Alhajin Kaulaha), Malam Tanimu Mai Rawani sune suka gabatar da addu'ar.
Malaman sun yi kira ga al'ummar Musulmi baki daya ko mene ne fahimtarka da a zo a hada kai domin a fuskanci matsalar tsaron don magance shi.
A karshe an yi addu'a Allah ya rusa duk masu hannu akan ta'addacin.
No comments