MATSALAR TSARO: An Tura Mata 'Yan Civil Defence Su Kare Makarantu Daga Harin 'Yan BindigaDaga Zaharaddeen Gandu

Hukumar tsaro ta Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a Najeriya, ta sanar da tura dakarunta mata, domin kare makarantu daga hare-haren 'yan fashin daji masu satar ɗalibai a jihohin ƙasar.

Kwamandan hukumar, Ahmed Audi, shi ne ya bayar da umarnin tattara su a ranar Laraba da ba su horo na wata ɗaya da kuma ba su kayan aiki a dukkan jihohin ƙasar guda 36, tare da Abuja.

Ya ce "tura dakarun wani ɓangare ne na shirin tsare makarantu na Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, da kuma Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola, wanda ya umarci kwamandan da ya fito da tsari don kawo ƙarshen matsalar".

"Biyo bayan yawaitar hare-hare da kuma garkuwa da ɗalibai a makarantu a ɓangarorin ƙasar nan, NSCDC ta yi wani nazari kan makarantu a faɗin ƙasar nan", a cewar wata sanarwar

Sanarwar ta ƙara da cewa "bayanan da muka samu za su taimaka wa dakaru wajen gudanar da aikinsu."

Dubban ɗalibai ne da malamansu 'yan bindiga suka sace daga makarantu, musamman a yankin Arewacin Najeriya tun daga Disamban 2020.

Post a Comment

0 Comments