MATSALAR TSARO: Za A Yi Sallar Alkunuti A Zariya


Daga Muhammad Farouk

Sakamakon yadda matsalar tsaro da garkuwa da jama'a ya yi kamari a garin Zariya ta jihar Kaduna, Malamai dake zaune a Unguwar Kusfa Zariya sun kira taron gangamin sallar Alkunuti domin kai kuka ga Allah ya kawo musu dauki.

Salman Zaria, wani mazaunin garin na Zariya ne ya tabbatar da hakan kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce; "Malaman Kusfa Zaria City suna gayyatar al'umma zuwa sallar al'qunut saboda hare-hare na masu garkuwa da mutane wanda za a yi a Azaran Dabuwa Kofar Gayan Low Cost da misalin karfe 8 na safe  Allah yayi mana maganinsu".

Garin na Zariya a jihar Kaduna na fama da hare-haren masu garkuwa da jama'a. Inda aka jera kwanaki takwas a jere 'yan bindigar na kai hare-hare.

A jiya Litinin ma Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka bisa yadda 'yan bindigar ke ci gaba da yi wa masarautarsa kofar rago. 

Post a Comment

0 Comments