Matsalar Tsaro A Zariya: Al'umma Sun Amsa Kira An Yi Sallar Alkunuti


Daga Aqil Abdulkadir

Da safiyar yau Laraba ne al ummar Musulmi suka amsa kiran da Malaman Kusfa a Zariya suka yi na a fito domin gabatar da addu'a ta musamman duba da yadda rashin tsaro ya yi kamari a garin na Zariya ta jihar Kaduna.   

Bayan taruwar jama'a an gabatar da sallah raka'a biyu wanda Limamin makabarta  'ABIDIR RAHMAN' ya jagoranta.

Bayan idar da sallar Limamin ya yi nasihohi akan mutane su koma ga Allah da tuba, sannan ya yi addu'a. Daga nan mutum biyu sun yi. A karshe aka yanka raguna guda biyu domin neman dacewa.

Taron addu'ar dai ya tara al'umma maza da mata, yara da manya.

Sai dai al'umma da dama da MADOGARA ta tattauna da su sun koka kan rashin ganin ko mutum daya daga shuwagabannin al'umma na jihar. 

Post a Comment

0 Comments