Morocco Ta Halasta Noman Wiwi A Kasar
Bbc ta labarto cewa; majalisar dokokin Morocco ta amince da dokar da ta halatta samar da tabar wiwi a ƙasar don magani da kuma amfanin masana'antu.

Manufar matakin ita ce shiga kasuwar duniya da bunƙasa noma da samar da ayyukan yi a yankunan karkara.

Morocco tana ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu samar da tabar wiwi don haramtacciyar hanya, da kuma domin shakatawa. Wannan zai kasance ba bisa doka ba a ƙarƙashin sabuwar dokar.

Post a Comment

0 Comments