Mulkin Danniya Da Ake Yi Ya Sanya Na Fice Daga APC, Inji Sheikh Umar Kwangila



Daga Auwal Adam 

MADOGARA ta labarto cewa; wani matashin dan siyasa wanda ake gogayya da shi a cikin jam'iyyar APC ta karamar Hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, ya shelanta ficewarsa daga jam'iyyarsa bisa abin da ya kira da jam'iyyar na yi na; "rashin adalci, tsari, danniya, handama, babakere da mulkin kama karya da ta ke yi wa ƳaÆ´anya da ta haifa. Ba zan tsura ido ana zaluntar Al'umma ba na yi shiru, saboda kare muradun jam'iyya", ya wallafa. 

Matashin ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a shafinsa na Facebook, inda ya fara da cewa; "Ni Shiek Umar Kwangila halastaccen ÆŠan Jam'iyyar APC Mai Mulki. Daga yau 17th June, 2021 ina jaddada ficewa ta daga Jam'iyyar APC, sakamakon rashin adalci, tsari, danniya, handama, babakere da mulkin kama karya da ta ke yi wa ƳaÆ´an ta da ta haifa. Ba zan tsura ido ana zaluntar Al'umma ba na yi shiru, saboda kare muradun jam'iyya", ya tabbatar. 

Ya ci gaba da cewa; "A karshe ina nisanta kai na da duk wani abu da ya danganci APC tun daga Gunduma har Ƙasa baki ÆŠaya, kuma ina Æ™ara shaidawa Al'umma wannan hukunci na yanke shi ne bisa Æ™wararan dalilai, kuma mutumci da zumuncin da ke tsakanin mu da wasu ƳaÆ´an jam'iyyar APC ya na nan kama yadda ya ke, amma zan É—auki mataki akan duk wanda ya alÆ™anta Ni da APC", ya jaddada. 

Post a Comment

0 Comments