Mutane 53 Gwamnatin Zamfara Da Rundunar 'Yan Sanda Suka Amso Daga Masu Garkuwa


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara tare da hadin gwiwa da rundunar 'yan Sanda sun ceto mutane Hamsin da uku da masu garkuwa da mutane suka sace  a kauyen  'Yar  Katsina da ke cikin laramar Hukumar Bungudu.

Kwamishina tsaro da cikin gida na Jihar, Hon. Abubakar Dauran ya tabbatar da haka alokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Gusau.

Kwamishina Abubukar Dauran ya bayyana cewa, Sakamakon sulhu da gwamnatin ke yi da 'yan bindiga ya ba su nasara ceto mutane ba tare da biyan kudin fansa ba.

Kuma ya tabbatar da cewa, Gwamna Matawalle na iyaka kokarinsa na ganin an kawo karshe 'yan ta'adda da kuma ta'addancin da suke yi ma al'ummar jihar ta Zamfara.

Kwamishina Dauran ya jinjinawa Rundunar 'Yan Sanda Jihar Zamfara wajen ba su gagarumin tallafin yaki da 'yan bindiga da kuma ceto mutane ne da su ke kamawa.

Post a Comment

0 Comments