Mutum Dubu Goma Ne Za Su Amfana Da Tallafin Kiwon Lafiya A Karamar Hukumar Zariya


  
Daga Idris Umar Zariya

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, Honorabul Abas Tajuddin, ya kaddamar da bayar da tallafin kiwon lafiya ga jama’ar karamar hukumarsa ta Zariya a ranar 7 ga watan Yunin 2021.

Idan za ku iya tunawa Honorabul Abbas Tajuddin ya saba gabatar da tallafi a bangarori da dama don sauke nauyin da ya a wuyansa a matsayinsa na wakili.

Likitocin da za su duba marasa lafiya sune “Doctors On The Move Africa” ta karkashin hukumar “National Tuberculosis and Leprosy Training Center, Saye wato asibitin kula da masu Tarin Fuka dake saye.

Wakilinmu na daya daga cikin wadanda suka shaida kaddamar da bayar da tallafin.

Tun farko kamar yadda aka saba akan gayyaci manyan mutane masu ruwa da tsaki a harkar lafiya da ke karamar hukumar ciki har da sarakuna da limamai.

A wannan karon ma haka lamarin ya tabbata, yayin da dubban mutane suka hallara a asibitin da ke Lemu a cikin birnin Zariya don shaida kaddamar da bayar da tallafin. Honorabul Tajuddin shi ne babban bako a gurin taron.

Dakta Haruna Kigbu shi ya jagoranci ayarin likitocin da za su bayar da tallafin .

A jawabin dan majalisar wanda shi zai dauki dawainiyar bayar da shi tallafin, ya fara ne da yin godiya ga Allah madaukakin sarki da Ya bashi ikon sauke nauyin al’ummarsa, ya ce kuma wannan tallafin na daya daga cikin ayyukan mazabarsa wanda ba shi ne na farko ba akwai tallafi na karatu da koyar da sana’ar hannu ga matasa maza da mata da aka bayar a lokutan baya.

Dan majalisar ya kara sa cewa daga cikin ayyukan da ya ke gabatarwa ga al’ummarsa a bangarori da dama kamar al’amuran da suka shafi ilimi, bai wa matasa tallafin karatu da sana’a, ya ce harkar bayar da tallafin kiwon lafiya ya fi kwanta mashi a ransa don haka nema a wannan karo ya tsaya tsayin daka don ya ga an samu nasara a cikin al’amarin.

A wannan lokacin dan majalisar ya tabbatar da cewa za a duba mutane akalla kusan 10,000 a bangarori daban-daban.

Daga ciki akwai shirin duba masu matsalar idanu tare da yi masu aiki a bangare guda kuma akwai shirin duba masu fama da kaba da hawan jini. Sannan ya tabbatar da cewa za a bai wa dubbai gilashin ido bayan sun sami gwaji na musamman a bangaren.

Karshe ya roki alfarma ga dukkan jama’an da suka zo don karbar magani da su bi doka da oda da jami’an kiwon lafiyan suka tsara.


Daga cikin wadanda suka yi ta’aliki game da gudummuwar da dan majalisar ke bayarwa akwai shugaban asibitin tarin fuka na Zariya da daya daga cikin iyayen kasa wato Jarman Kudun Zazzau Alhaji Nuhu Aminu Bamalli da shi kansababban likitan da ke aikin. Dakta Kigbu, inda suka ce Honorabul Tajuddin mutumne mai kokari da son kawowa jama’arsa ci gaba don haka sun roki jama’ar kasar Zazzau dasu ci gaba da bashi goyan baya

Karshe sun yi fatan alkhairi a gare shi tare dan neman Allah Ya sa mashi hannu a dukkan abubuwan da ya sa gaba.

Wakilinmu ya zanta da wasu daga cikin wadanda suka amfana da wannan tallafi. Malam Muhammad Haruna, dan shekara 51, da yake fama da ciwon Idanu mazaunin Unguwar Kwarbai cikin Zariya ya nuna jin dadinsa matuka yayin da ya samu gilashi da magani, ya kuma yi fatan Allah Ya biya wa dan majalisar bukatunsa bakidaya.

Akwai kuma Hajiya Aisha Abdullahi   da ke fama da ciwon mara tuni har an yi mata awo an rubuta mata magunguna wasu daga cikin danginta sun nuna jin dadinsu bisa yadda suka ga ana kula da ‘yar uwartasu kuma da alamar nasara a cikin lamarin yanzu haka.

Ya zuwa hada wannan rahoto, jama’a ne ke dafifi a asibitoci 2 wato tsohon asibitin ABU dake Tudun Wada da Asibiti gwamtin dake Lemu Zariya inda  ake bayar da tallafin ka’in da na’in.

A bangare guda kuma, al’ummar Karamar Hukumar Zariya ne ke nuna jin dadinsu game da yadda dan majalisar ke bayar da gudummuwarsa a bangarori da dama kuma sun nuna jin dadinsu tare da yi masa fatan Allah Ya biya masa bukatarsa kuma sun yi kira ga sauran ‘yan majalisu su yi koyi da halinsa, suka ce hakan zai kawo cigaba a kasa. Sun yi fatan Allah Ya zaunar da kasa lafiya ya kare jam’iyyar APC.

-Leadership A Yau

Post a Comment

0 Comments