Nan Da 2030 Yawan 'Yan Kwaya A Nijeriya Zai Kai Miliyan 20, Inji Majalisar Dinkin Duniya

 


Rfi Hausa ta labarto cewa; ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake sa ido kan tu’ammuli da miyagun kwayoyi gami da laifuka masu alaka da su UNODC, ya ce ‘yan Najeriya fiye da miliyan 14 da dubu 300 ne suka zaman 'yan kwaya bayan sha na’u’ikan kwayoyi daban daban a shekarar 2020.

Kididdigar ta bayyana cewa kimanin kashi 5.5 cikin 100 na yawan al’ummar Najeriya tsakanin masu shekaru 15 zuwa 64 sun yi tu’ammuli da akalla na’u’in kwaya guda a shekarar da ta gabata.

Wadannan alkaluma na kunshe cikin rahoton da Majalisai Dinkin Duniya ke fitarwa duk shekara kan yadda ake sha da kuma fasakaurin miyagun kwayoyi a fadin duniya.

Rahoton ya bayyana annobar Korona a matsayin daya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa karuwar shan miyagun kwayoyi tsakanin mutane la’akari da dokokin kullen da suka shafe tsawon lokaci a ciki, bayan matakin hana zirga-zirgar jama’ar da hukumomi suka dauka domin dakile yaduwar cutar.

Wani hasashe Da Majalisar Dinkin Duniyar tayi ya ce adadin masu shan miyagun kwayoyi a Najeriya zai karu zuwa mutane miliyan 20 nan da shekarar 2030.

A shekarar da ta gabata kadai dai mutane miliyan 257 suka sha nau’ikan miyagun kwayoyi daban daban a fadin duniya, yayinda wasu miliyan 36 cikinsu miliyan 3 a Najeriya ke fama da cutukan tabin kwakwalwa saboda muggan kwayoyin.


Post a Comment

0 Comments