Nijeriya Za Ta Karbi Karin Allurar Rigakafin Korona Miliyan 4 Kyauta

 


Nijeriya za ta karbi karin taimakon allurar rigakafin cutar korona kyauta a karkashin shirin Covax da yawan sa ya kai miliyan 4 nan da watan Agusta mai zuwa.

Shi dai wannan shirin tallafin Covax an shirya shi ne domin taimakawa kasashe matalauta wajen ganin sun samu damar yiwa al’ummar kasashen su miliyan 80 daga cikin kasashe da yankuna 129 na duniya rigakafin cutar.

Nijeriya mai dauke da mutane sama da miliyan 200 ta karbi kashi na farko na maganin rigakafin cutar samfurin AstraZeneca a watan Maris wanda tuni aka yiwa wasu daga cikin jama’ar ta allurar kamar yadda Rfi Hausa ta labarto.

Shugaban Hukumar kula da lafiya a matakin farko Dr Faisal Shuaibu ya kuma bayyana cewar gwamnatin kasar za ta sayi maganin rigakafin kirar Johnson & Johnson kusan miliyan 30 ta hannun kungiyar kasashen Afirka ta AU da AfreximBank nan da watan Satumba mai zuwa, bayan kammala amfani da allura kusan miliyan 4 a matakin farko.

Shuaibu ya bukaci masu jan kafa wajen karbar allurar da su kauda duk wani shakku da suke da ita wajen gabatar da kan su domin yi musu rigakafin wanda yace bashi da wata illa.

Cutar korona ta hallaka mutane 2,119 daga cikin 167,467 da aka tabbatar sun harbu da ita a Najeriya.


Post a Comment

0 Comments