RASHIN TSARO: Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugabannin Tsaro A Abuja


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci ganawar gaggawa da shugabannin tsaron kasa a babban birnin tarayya Abuja.  

Taron dai shi ne irinsa na farko tun bayan nada  Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojan kasa ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata.

A ranar Litinin ne dai Janar Farouk ya kai wa shugaba Buhari ziyara. 

Wadanda suka halarci taron dai sun hada da shugaban kasa Muhammad Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo. 

Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da mai bawa shugaban kasa Shawara a kan harkokin tsaro Babagana Monguno da sauransu.

Post a Comment

0 Comments