Rashin Tsaro Ya Shiga Jihar Kebbi; Mahara Sun Kashe Mutum 88

 


Daga Muhammad Farouk 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi a ranar Asabar sun tabbatar da cewa mahara sun kashe mutum 88 a karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar a ranar Alhamis. 

Jami’in hulda da jama’a da rundunar ‘yan sandan, DSP Nafi’u Abubakar ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce dukkanin wadanda aka kashe an kashe su ne a kauyuka takwas a tsakanin karamar hukumar. 
A cewarsa ya zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan sun kwaso gawarwaki 88 inda suka raba jami’ansu domin dawo da doka da oda a kauyukan da lamuran ya shafa. 

 “an yi kashe-kashen ne a kauyukan Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iguenge duka a karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi’, inji shi.

 “da farko gawarwakin da muka tsinto guda 66, amma da nake Magana da kai yanzu gawarwakin guda 88 ne aka gano,” inji Abubakar.

Idan ba ku manta ba a cikin watan Afrilun shekararnan ma ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda 9 a yankin ciki harda DPO a lokacin da suka kai wa kauyukan dauki. 

Post a Comment

0 Comments