Hukumar Bunkasa Noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta yi gargadi game da karancin abinci a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya. FAO ta...
Hukumar
Bunkasa Noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta yi gargadi game da karancin
abinci a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.
FAO
ta ce matsalar Boko Haram ta hana manoma kimanin dubu 65 da 800 samun gudanar
da ayyukan gona a yankin.
Wakilin
FAO a Nijeriya, Fred Kafeero ne ya bayyana haka yayin bikin kaddamar da ayyukan
noman rani na wannan shekara a Maiduguri.
Rahoto
kan halin da noma ke ciki a Arewa maso Gabashin Nijeriyar na zuwa ne a daidai
lokacin da mazauna karamar Hukumar Kala Balge a Jihar Borno ke kokawa kan yadda
Giwaye suka addabi ayyukansu na noma, kamar yadda Kaumi Ali Ngalama ya shaidawa
sashin Hausa na RFI.
No comments