Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda rikicin shekaru 12 da yankin arewa maso gabashin Nijeriya ya fuskanta ya lakume rayu...
Wani
rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda rikicin shekaru 12 da yankin
arewa maso gabashin Nijeriya ya fuskanta ya lakume rayukan kananan yara dubu
dari 3 da 24 galibinsu wadanda shekarunsu ya fara daga biyar zuwa kasa.
Rahoton
ya bayyana cewa, alkaluman kari ne kan mutum dubu 40 da hare-haren Boko Haram
ya kashe daga shekarar 2009 zuwa yanzu baya ga wasu mutum miliyan 2 da rikicin
ya raba da muhallansu.
Rahoton
na Majalisar Dinkin Duniya ya ce galibin kananan yaran sun mutu ne sanadiyyar
cutukan da ke musu barazana ciki har da kyanda baya ga yunwa da rikicin na Boko
Haram ya haddasa tsanantarta a yankin.
Rahoton
na Majalisar Dinkin Duniya wanda aka yiwa take da ‘‘Illar da rikici ya haifarwa
ci gaban yankin arewa maso gabashin Nijeriya’’, ya ce kashi 90 na wadanda
rikicin shekarun 12 ya salwantar da rayukansu kananan yara.
Sashen
shirin bunkasa birane na Majalisar da ya jagoranci fitar da rahoton, ya ce
rikicin na Boko Haram ya kassara harkokin Noma da cinikayya da kuma samar da
abinci wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen haddasa yunwa tsakankanin biranen da
suka dogara da yankin.
A
cewar sashen akwai sauran illolin da yakin na shekaru 12 ya haifarwa yankin
baya ga kisan daruruwan mutanen da kuma wadanda suka rasa matsugunansu.
No comments