Gwamnatin Jihar Gombe ta ce rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummar Shongom da Filiya game da gona ya yi sanadiyyar kashe mutum ɗaya tare ...
Gwamnatin Jihar Gombe ta ce rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummar Shongom da Filiya game da gona ya yi sanadiyyar kashe mutum ɗaya tare da ƙona gidaje kusan 50 a jihar.
Kwamishinan YaÉ—a Labarai Julius Ishaya ne ya bayyana hakan jim kaÉ—an bayan wani taron majalisar tsaro a Gombe ranar Litinin.
Ya bayyana cewa rikicin wanda ya auku ranar Asabar, 29 ga watan Mayu, ya yi sanadin mutuwar wata mata sannan aka ƙona gidajen mutane kusan 50, wanda suka ƙunshi sauran kayan amfani kamar abinci.
Ishaya ya ce gwamnati ta yi Allah-wadai da harin kuma tana kiran al'ummomin biyu da su zauna lafiya tare da yin zaman sulhu ƙarƙashin jagorancin Mai Kaltungo, Saleh Mohammed, domin dawo da zaman lafiya.
No comments